Rundunar sojojin Isra’ila ta ce ta janye daga asibitin al-Shifa da
ke birnin Gaza bayan wani samame na tsawon mako biyu,
wanda ya yi raga-raga da galibin gine-ginen asibitin.
A cewar rundunar tsaron sojin Isra’ila, dakarun ƙasar sun hallaka ‘yan ta’adda kuma sun gano ɗumbin makamai da bayanan ayyukan sirri” a yankin.
Samamen ya faru ne bayan Isra’ila ta ce ta samu bayanan sirrin da ke nuna cewa Hamas na amfani da asibitin a matsayin wani sansanin ƙaddamar da hare-hare.
Hamas dai ta musanta amfani da cibiyoyin lafiya don gudanar da ayyukan sojoji. A cikin ‘yan makonnin nan, an ba da rahoton ɓarkewar ƙazamin faɗa a zagayen asibitin, wanda shi ne mafi girma a Gaza.