Home Home Minista Sadiya Ta Miƙa Ragamar Ma’aikatar Harkokin Jinƙai Ga Babban Sakatare

Minista Sadiya Ta Miƙa Ragamar Ma’aikatar Harkokin Jinƙai Ga Babban Sakatare

486
0

Ministar Harkokin Jin-ƙai da Agaji Sadiya Farouq, ta miƙa ragamar gudanar da ayyukan ma’aikatar ga Babban Sakataren ma’aikatar Dakta Nasir Sani Gwarzo bayan ta kammala aikin ta cikin nasara.

Hajiya Sadiya ta riƙe ma’aikatar ne a matsayin minista ta farko na tsawon shekaru uku da rabi, inda ta yi wa al’umma aiki tuƙuru babu gajiyawa.

Sadiya ta miƙa wasu takardu ƙunshe a cikin kundaye biyu da ke bayyana ayyukan da ta yi a ma’aikatar, a ƙarshen wani Taron Duniya a kan Ayyukan Agaji na Nijeriya karo na farko da ma’aikatar ta ɗauki nauyin shiryawa a Abuja.

A jawabin ta, ministar ta gode wa Babban Sakataren da daraktoci da ma’aikatan ma’aikatar da na ofishin ta bisa gagarumin goyon bayan da su ka ba ta a tsawon wa’adin riƙe muƙamin ta.

Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta kuma yi kira ga ma’aikatan su tsaya tsayin-daka a kan ƙoƙarin da su ke yi na ganin an cimma nasara a muradin Shugaba Buhari na ‘yanto ɗimbin marasa galihu daga ƙangin fatara da yunwa.

LEAVE A REPLY