Home Home An Hana Ganduje Shiga Wurin Manyan Baki A Filin Rantsar Da Tinubu

An Hana Ganduje Shiga Wurin Manyan Baki A Filin Rantsar Da Tinubu

273
0

Tsohon Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya gamu da cikas a wajen bikin rantsar da sabon Shugaban Kasa da ya gudana a dandalin Eagle Square da ke Abuja.

Ganduje da matar sa Hafsat dai sun yi kokarin shiga wurin da aka kebe wa manyan baki masu alfarma, amma sai jami’an tsaro su ka dakatar da su.

Jami’an tsaron sun yi wa Ganduje bayanin cewa, takardar gayyatar da ya ke da ita koriya ce, kuma sai mai takardar gayyata mai ruwan Gwal ne zai shiga bangaren.

Rahotanni sun ce, Ganduje da matar sa sun yi Cirko-Cirko na tsawon fiye da mintina 10, kafin su dauki kaddara su koma bangaren da aka tanadar wa baki irin sa.

Haka kuma, gwamnan Jihar Anambra Charles Soludoya yi kokarin shiga bangaren, amma kamar Ganduje shi ma jami’an tsaro sun taka ma shi birki.

Leave a Reply