Home Labaru Kasuwanci Mele Kyari: Moriyar Da ‘Yan Arewa Za Su Ci Daga Dokar Mai...

Mele Kyari: Moriyar Da ‘Yan Arewa Za Su Ci Daga Dokar Mai Ta PIB

12
0

Shugaban kamfanin mai,NNPC a kasa NNPC ya ce duk da cewa dukkannin ‘yan Najeriya za su mori dokar PIB amma arewacin kasar zai fi kowa samun moriyar dokar.

Ana sa ran cewa sabuwar dokar ta mai ta PIB za ta yi wa kowanne ɓangare da ya shafi harkar mai a Najeriya garambawul.

A watan Agusta ne dai Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba wa dokar man fetur ta Petroleum Industry Bill (PIB) hannu bayan majalisun dokokin kasa sun amince da ita a watan Yuli.

An shafe fiye da shekaru 20 ana ce-ce-ku-ce a kan dokar. Sai dai duk da sukar da wasu ƴan ƙasar ke yi mata, shugaban kamfanin mai na kasa (NNPC), Alhaji Mele Kyari, ya kare dokar da cewa tana da matuƙar muhimmanci ga ‘yan Najeriya musamman ma yankin arewacin kasar.

Dangane kuma da ribar makudan kudi da kamfanin NNPC din ya samu irinta ta farko a shekaru kusan 50, shugaban na NNPC ya ce “hakan ya samu ne sakamakon goyon bayan da shugaban Buhari ya bai wa kamfanin.”