Home Labaru Kasuwanci Tsadar Rayuwa: Abin Da Ya Sa Gas Din Girki Tashin Gwauron Zabo...

Tsadar Rayuwa: Abin Da Ya Sa Gas Din Girki Tashin Gwauron Zabo -NNPC

143
0

Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) ya ce karancin gas din da ake samarwa a Najeriya ne ya sa farashin gas din girki, yayi tashin gwauron zabo a kasar.

Shugaban NNPC, Mele Kyari, ne ya bayyana haka, yana mai cewa kamfanin na yin iya kokarinsa domin ganin farashin gas din girki ya sauka.

Da yake bayyana hakan a lokacin ziyarar sa ga ofishin Hukumar Kula da Albarkatun Mai ta Kasa (DPR) a ranar Talata, Mele Kyari ya kuma danganta matsalar da raunin hanyoyin samar da gas din girki a kasar suka yi.

A cewarsa, hakan ne ya sa yanzu NNPC din take aiki tare da sauran hukumomi masu alaka da ita don ganin ana samar da isasshen gas din girki saboda masu amfani da shi a gida da ’yan kasuwa su rika samun sa cikin sauki kuma a kusa da su.

Mele, ya ce matakan za su fadada hanyoyin samar da gas din ta yadda za a isar da su zuwa gidaje.

Ya bayyana cewa samar da wadatacciyar iskar gas zai taimaka wajen samun ingantacciyar wutar lantarki mai dorewa, wadda kuma ta fi sauki.

Leave a Reply