Matashin dan wasan gaba na Faransa da ke taka leda da PSG, Kylian Mbappe ya bayayan cewa yana kishin ruwar ganin sa a wani muhalli daban sabanin inda ya ke yanzu, kalaman da kai tsaye ke fayyacewa yiwuwar aski ya zo gaban goshi game da shirye-shiryen sauya shekar sa.
A karshen wannan kaka kwantiragin Mbappe mai shekaru 22 zai kare da PSG kuma akwai kwararan bayanai da ke nuna cewa ya na shirin komawa Real Madrid ne ta Spain da taka leda.
A cewar Mbappe ya na fatan fuskantar sabon kalubale nan gaba kadan, haka zalika a kage ya ke ya hadu da sabbin abokan wasa.
Dan wasan ya bayyana cewa fuskantar sabon kalubale a rayuwa ya fi masa muhimmanci fiye da tara dimbin dukiya a PSG.














































