Mazauna birnin Enugu sun yi watsi da umarnin da gwamnan
jihar ya bada, na bijire wa umarnin ƙungiyar IPOB na zaman
gida a ranar Litinin.
Rahotonni sun ce tituna da makarantu da bankuna da kasuwanni da sauran wuraren gwamnati ke ci-gaba da kasancewa babu kowa.
Idan dai za a iya tunawa, a ranar 1 ga watan Yuni ne gwamnan jihar Peter Mbah ya yi iƙirarin cewa, daga yanzu ya haramta batun zama a gida da ƙungiyar IPOB ta bada, inda ya umurci al’umma da ɗaiɗaikun ƙungiyoyi a faɗin jihar su fita harkokin su na yau-da-kullum.
Gwamna Mbah, ya ce gwamnatin shi a shirye ta ke ta tattauna da mutanen da ke da kyayyawar aniyar samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali domin tabbatar da tsaro da zaman lafiyar jihar.
Kungiyar IPOB dai ta kwashe watanni ta na kakaba dokar zaman gida a wasu ranaku a yankin kudu maso gabashin Nijeriya, a wani mataki na neman sakin jagoran ƙungiyar Nnamdi Kanu, wanda masana tsaro ke kallo a matsayin babbar barazana ga tsaron Nijeriya.














































