Home Labaru Matsin Lamba: Akwai Yiwuwar Sayar Da Kungiyar Kwallon Kafa Ta Manchester United

Matsin Lamba: Akwai Yiwuwar Sayar Da Kungiyar Kwallon Kafa Ta Manchester United

106
0

Akwai yiwuwar sayar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United bayan shafe shekaru 17 karkashin iyalin Glazer, a dai dai lokacin da kungiyar ke fuskantar matsin lamba daga magoya baya.

Glazer( Mai Manchester United)

Rahotanni na cewa iyalin Glazer na shirye shiryen sanar da aniyar sayar da kungiyar a hukumance ta wajen neman karin masu zuba jari.

Yanzu haka dai iyalan na Glazer sun tuntubi kwararru a fannin zuba jari don neman shawarwari a kan yadda za su tafiyar da wannan sabga.

An ji wani daga cikin kwararrun ya na ikirarin cewa nan bada jimawa ba wata sanarwa za ta fito daga masu kungiyar a don karin haske a game da matsayin na su.

Wannan na zuwa ne jim kadan bayan da kungiyar ta tabbatar da cewa za ta rabu da dan wasanta mai girma, wato Cristiano Ronaldo bayan da ya caccaki manyan ja

Leave a Reply