Home Labaru Matsalar Tsaro: ‘Yan Bindiga Sun Salwantar Da Rayuka 10 A Jihar Katsina

Matsalar Tsaro: ‘Yan Bindiga Sun Salwantar Da Rayuka 10 A Jihar Katsina

729
0

Rahotanni sun tabbatar da cewa, rayukan mutane 10 sun salwanta, yayin da mutane biyar su ka jikkata kamar yadda hukumomin tsaro su ka bayyana, sakamakon wani mummunan hari da ‘yan bindiga su ka kai a kauyen Kirtawa da ke karamar hukumar Safana ta jihar Katsina.

‘Yan bindigar, sun kuma kone kimanin motoci biyar da babura hudu tare da satar dimbin shanu yayin aukuwar lamarin.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Katsina SP Gambo Isah ne ya bada tabbacin mummunan lamarin, yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Katsina SP Gambo Isah

SP Gambo, ya kuma bada tabbacin jikkatar wani jami’in soji da hukumar tsaro ta Civil Deffence yayin artabu da ‘yan bindigar.

Yayin jajentawa iyalan wadanda lamarin ya shafa, SP Gambo ya ce ‘yan bindigar sama da 300 ne su ka kai mummunan hari da misalin karfi 5.20 na Yammacin ranar Asabar da ta gabata.
0