Home Labaru Mutuwar Funke: Gani Adams Ya Ce A Saurari Abin Da Zai Biyo...

Mutuwar Funke: Gani Adams Ya Ce A Saurari Abin Da Zai Biyo Baya

416
0

Shugaban kungiyar Yarabawa ta OPC Gani Adams, ya ce kada wani ya ce uffan idan su ka dauki fansar kisan ‘yar shugaban kungiyar Yarabawa ta Afenifere da ake zargin masu garkuwa da mutane ne su ka yi a Akure.

Shugaban kungiyar Yarabawa ta OPC Gani Adams

Gani Adams, ya ce sun dade su na jan hankalin gwamnatocin yankin jihohin Yarabawa cewa fulani sun addabe su amma su na yin shiru, ya na mai cewa yanzu tura ta kai bango, suna so su gaya wa duniya cewa an kure su, don haka duk abin da suka yi kada a zarge su ko a ga laifin su.

Ya ce ba wai ba su san yadda za su tunkari abin su kawo karshen sa ba ne, amma yanzu an taba na su, kuma kada wani ya yi tunanin za su yi shiru ne ba tare da daukar mataki ba.

Gani Adams ya cigaba da cewa, za  su jira rahoton ganawar da gwamnonin yankin su ke yi a kan tsaro, kuma lallai a saurare su nan ba da dadewa ba.

Leave a Reply