Uwargidan Shugaban Kasa Sanata Oluremi Tinubu, ta tallafa
ma wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a rukunin gidaje na
TradeMore da ke Abuja da Naira dubu 250 kowannen su.
Da ta ke jawabi a karkashin shirin ta mai suna Renewed Hope Initiative a Turance bisa wakilcin matar Mataimakin Shugaban Kasa Nana Shettima, Oluremi ta bayyana alhinin ta ga mutanen da Ibtila’in ya shafa.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ta Busola Kukoyi ya fitar, Remi ta ce duk da babu tabbacin ambaliyar ba za ta sake faruwa ba tunda har yanzu ana cikin damina, amma ta na fatan taimakon zai rage masu radadin da su ke ciki.
Ta ce duk da cewa har yanzu ta na kan aikin yi wa shirin ta rajista da gwamnati, amma ba zai yiwu ta zuba wa mutanen ido ta na kallon su kawai ba.