Home Labaru Matakai 12 Da Shugaba Tinubu Ya Dauka Na Wadata Nijeriya Da Abinci

Matakai 12 Da Shugaba Tinubu Ya Dauka Na Wadata Nijeriya Da Abinci

42
0

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bada umarnin maida
duk al’amurran da su ka jibinci samar da abinci a karkashin
kulawar majalisar tsaro ta kasa.

Ya ce sun ayyana dokar ta-baci tare da kaddamar da wani babban shiri na samar da wadataccen abinci da saukin sa tare da daukar sahihan matakai domin magance hauhawar farashi.

Matakan da shugaba Tinubu ya ce gwamnati za ta bi domin tabbatar da wadatar abinci a Nijeriya, sun hada da ba manoma da magidanta taki da tsabar hatsi ba tare da bata lokaci ba, da da Kirkirar Hukumar Kula da Kayan Abinci domin bin diddigin farashi da kula da muhimman wuraren adana kayayyakin abinci

Sauran sun hada da Karfafa matakan tsaro ga manoma da gonaki, da Farfado da eka dubu 500 ta kasa domin noma da kuma koguna don a ci-gaba da noman rani, da Bunkasa bada jari da kudade ga fannin noma, da Inganta sufuri da wuraren ajiyar kayayyakin abinci.

Akwai kuma Kara yawan kudaden shiga daga harkar fitar da abinci da albarkatun noma wasu kasashen, da Inganta harkokin kasuwanci ta hanyar aiki da hukumar fasa-kwauri ta Nijeriya, da Samar da dimbin ayyukan yi a fannin noma, da kuma Maida hankali wajen tabbatar da cewa kowanne dan Nijeriya ya samu abinci a kan farashi mai sauki.

Leave a Reply