Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da kwamitin inganta tattalin arzikin kasa NEC na 2019 zuwa 2023.
Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranci rantsarwa a dakin taro na fadar shugaban kasa da ke abuja wanda ya samu halartar daukacin gwamnonin jihohi Nijeriya.
Taron rantsarwar ya samu halartar sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari da Gwamnan babban bankin Nijeriya CBN Godwin Emefiele da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Babagana Monguno.
Sauran wadan da suka latarci taron sun hada da gwamnonin jihohin Lagos da Niger da Nasarawa da Ekiti da Borno da Ondo, Kano da Jigawa da Kebbi da Kwara da Kaduna da dai sauran su.
A jawabin da ya gabatar a lokacin taron, mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya ce kwamitin na da muhimmanci sakamakon nauyin da aka daura mashi na bayda shawarwari da kirkiro dabarun ciyar da tattalin arzikin kasa gaba.
A karshe shugaba Buhari ya bukaci ‘yan kwamitin su bada fifiko a kan fanonin tsaro da ilimi da noma da kuma kiwon lafiya, sannan ya ce nasarorin da za a samu a bangarori za su taimaka wajen daga darajar rayuwar ‘yan Nijeriya.