Home Labaru Kiwon Lafiya Yaki Da Tu’ammuli: NDLEA Ta Ce Jihar Ta Fi Kowacce Jihar A...

Yaki Da Tu’ammuli: NDLEA Ta Ce Jihar Ta Fi Kowacce Jihar A Arewa Safarar Kwayoyi

561
0

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta ce jihar Kwara ce ta farko a sahun jihohin arewacin Nijeriya  da aka fi safarar miyagun kwayoyi.

NDLEA ta gargadi ‘yan Nijeriya su gi safara da amfani da miyagun kwayoyi tare da yin kira ga al’umma su kasance masu biyayya ga dokokin kasa.

Babban jami’in hukumar Dandi Emmanuel ya bayyana haka ga manema labarai jim kadan bayan kammala taron hadin gwuiwa da wani kwamitin yaki da shan miyagun kwayoyi ya shirya a jihar Kwara.Emmanuel ya kara da cewa, hukumar NDLEA ta kama mutane 91 da laifukan safarar miyagun kwayoyi da suka hada da tabar wiwi da wasu kwayoyi daban-daban masu dumbin yawa a tsakanin watan Yuli na shekara ta 2018 zuwa yanzu.

Leave a Reply