Home Labaru Mataki: Majalisar Zamfara Ta Sanar Da Mataimakin Gwamna Mahdi Cewa Za Ta...

Mataki: Majalisar Zamfara Ta Sanar Da Mataimakin Gwamna Mahdi Cewa Za Ta Tsige Shi

115
0
Babbar alkalin Jihar Zamfara Mai Shari'a Kulu Aliyu, ta rantsar da kwamatin mutum biyar da zai binciki laifukan da ake zargin Mataimakin Gwamna Mahdi Aliyu Gusau na rashin ɗa'a.

Majalisar Jihar Zamfara ta ce ta aika wa mataimakin gwamnan jihar Mahdi Aliyu Gusau sanarwar cewa za ta tsige shi daga mukaminsa.

Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar Shamsudeen Hassan ya shaida wa tashar talabijin ta Channels wannan labarin a Gusau, babban birnin jihar ta Zamfara.

Ya ce majalisar za ta tsige mataimakin gwamnan daga mukaminsa ne saboda tuhumar da suke yi masa cewa ya aikata laifuka karkashin sashe na 190 da 193 na tsarin mulkin Najeriya.

Majalisar ta kuma tuhumi Mahdi Aliyu Gusau da azurta kansa da kudin al’umma ta haramtacciyar hanya bayan da ta ce ya karkatar da kudaden jihar ga wasu bukatun kansa, baya ga kitsa wani shiri na damfarar jihar.

Yayin da mataimakin gwamnan ke cewa bai aikata wani laifi ba, majalisar ta ce ta aika wa Mahdi Aliyu Gusau sanarwar tsige shin ta hannun sakataren gwamnan jihar ne.