Home Labaru Mataimakin Gwaman Jihar Anambra Ya Koma Jam’Iyyar APC  

Mataimakin Gwaman Jihar Anambra Ya Koma Jam’Iyyar APC  

13
0

Mataimakin Gwamnan Jihar Anambra Nkem Okeke ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC, har shugaban kasa Muhamamdu Buhari ya karbi bakuncinsa.

Sauya shekar mataimakin gwamnan na Anambra daga jam’iyyar APGA zuwa APC na zuwa ne kimanin mako biyar kafin zaben gwamnan jihar da za a gudanar a ranar 5 ga watan Nuwamba.

Shugaban rikon Jam’iyyar APC, Mai-Mala-Buni, ya jagoranci Mista Okeke zuwa Fadar Shugaban Kasa domin ganawa da shugaban kasa Buhari.

Mataimakin gwamnan Jihar ya samu rakiyar Gwamnan Jihar Imo, Sanata Hope Uzodinma, wanda shi ma dan jam’iyyar APC ne, a ziyarar da suka kai wa Buhari.