Home Labaru Iftila’i: Mutum 5 Sun Mutu A Gobarar Tankar Man Fetur A Adamawa

Iftila’i: Mutum 5 Sun Mutu A Gobarar Tankar Man Fetur A Adamawa

19
0

Mutum biyar sun mutu sakamakon gobarar tankar dakon mai a garin Mubi da ke arewacin jihar Adamawa a Najeriya.

Shaidu sun shaida cewa gobarar ta tashi ne daga gidan mai a sanyin safiyar Laraba lokacin da ake kokarin juye mai daga tankin mota zuwa daruruwan jarkoki a Kasuwan Gyela.

Garin Mubi da ke kan iyaka yankin ne da ake yawaita fasakaurin man fetur a kananan jarkoki cikin dare zuwa Kamaru.

Wani mazaunin yankin Habu Garba ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa akalla mutum biyar suka kone kurumus yayinda wasu da dama suka jikkata.

Wani mai aikin sa-kai, Adamu Madobi, ya ce ya halarci jana’izar ‘yan uwan juna maza uku da suka mutu sakamakon gobarar.

Sannan ya kara da cewa akwai babura masu kafa uku guda 50 da suka lalace a gobarar.

A lokacin tabbatar da aukuwar iftila’in, shugaban hukumar agajin gaggawa ta SEMA reshan jihar, Dakta Muhammad Sulaiman ya shaida cewa mutum 3 sun mutu yayinda wasu biyu ke karbar kulawa a asibiti.