Home Labaru Masu Suka Kan Rufe Iyakoki Sun Dawo Suna Yaba Min – Shugaba...

Masu Suka Kan Rufe Iyakoki Sun Dawo Suna Yaba Min – Shugaba Buhari

12
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce ‘yan Nijeriyar da
su ka rika sukar sa saboda rufe iyakokin kasar nan daga
karshe sun dawo su na yabon sa.

Buhari ya ce ya dauki matakin rufe iyakokin ne domin karfafa wa ‘yan Nijeriya gwiwa a kan samar da abincin da su ke bukata.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne, lokacin da ya ke kaddamar da sabon ginin helkwatar hukumar hana fasa- kwauri ta Nijeriya a yankin Maitama da ke birnin tarayya Abuja.

Ya ce ya na sane ya bada umarnin a rufe iyakokin saboda ya san ‘yan Nijeriya su na sayo shinkafa daga waje su ba Nijar da wasu kasashe sannan su shigo da saura.

Shugaban Buhari, ya ce arzikin da Nijeriya ta ke da shi na mutane da kasa da kuma yanayi, kasashe ‘yan kadan ne a duniya su ke da shi.