Masu sha’awar wasannin kwallon kafa sun bukaci hamshakin attajirin Afirka Alhaji Aliko Dangote ya saka hannun jari a gasar firimiyar Najeriya domin cigaban wasanni a kasar sa.
Magoya bayan kwallon kafa a ciki da wajen Najeriya sun bayyana hakan ne ta shafukan sada zumunta na zamani,
A matsayin martani kan nadamar da hamshakin attajirin ya ce ya yi na rashin siyan ƙungiyar kwallon kafa ta Arsenal.
A wata hira da ya yi da wakilin Bloomberg Francine Lacqua a New York,
Dangote ya bayyana cewa ya rasa damar siyan Arsenal ne a lokacin da kungiyar ta kai kusan dala biliyan biyu amma a maimakon haka ya sadaukar da dukiyar sa wajen gina matatar mai a Najeriya.