Home Labaru Maslaha: Nijeriya Za Ta Dage Haramcin Da Ta Yi Kan Wasu Kungiyoyin...

Maslaha: Nijeriya Za Ta Dage Haramcin Da Ta Yi Kan Wasu Kungiyoyin Agaji

243
0

Hukumar kula da ayyukan jin-kai ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce Nijeriya ta yi alkwarin dage haramcin da ta yi wa wasu kungiyoyin agaji na kasa da kasa da ke aiki a arewa maso gabashin Nijeriya.

Sanarwar ta fito ne daga shugaban hukmar Mark Lowcock, inda  ya ce ya gana da masu ruwa da tsaki da kuma hukumomin tsaron Nijeriya game da lamarin.

Idan dai ba a manta ba, a cikin watan Satumba, rundunar sojin Nijeriya ta rufe wasu ofisoshin kungiyoyin agaji, lamarin da ya sa ake fargabar cewa matsalar jin-kai za ta ta’azzara.

Rundunar sojin dai ta zargi kungiyar ta kasar Faransa da taimaka wa ayyukan ta’addanci, ta fuskar sama wa ‘yan ta’adda abinci da magunguna.

Lowcock, ya ce rikicin baya-bayan nan ya raba sama da mutane dubu dari da 40 da muhallan su, sannan ya jefa sama da miliyan 3 cikin hadarin rashin abinci sakamakon kasa noma da manoma su ka yi.