Jami’an ‘Yan sandan Nijeriya sun ceto mutane 108 da ke tsare a wata cibiyar kula da kangararru a jihar Kwara.
Kakakin ‘yan sanda na jihar Okansanmi Ajayi, ya ce sun kai samamen ne a cikin garin Illorin, inda su ka ceto maza 103 da mata 5, wadanda shekarun su ya kama daga 6 zuwa 45.
Samamen dai, shi ne na baya-bayan nan da ‘yan sanda su ka kaddamar a kan cibiyoyin gyaran halayyar kangararru a sassan Nijeriya.
A karshen watan Satumba, rundunar ‘yan sanda ta jihar Kaduna ta ceto kimanin mutane 300 da su ka hada da manya da kananan yara, wadanda ke tsare a wata makaranta da ke unguwar Rigasa da sunan koyar da tarbiya.
You must log in to post a comment.