Home Labarai Masha Allah: Ahmed Dangiwa Ya Kammala Aikin Da Shugaba Buhari Ya Ba...

Masha Allah: Ahmed Dangiwa Ya Kammala Aikin Da Shugaba Buhari Ya Ba Shi a FMBN

315
0

Shugaban bankin bada lamunin gidaje na Nijeriya Ahmed Musa
Dangiwa ya sauka daga mukamin sa, bayan wa’adin sa ya zo
karshe a makon da ya gabata.

Ahmed Dangiwa ya sanar da ajiye mukamin sa ne a wani sako
da ya wallafa a shafin sa na Twitter, inda ya ce ya damka
ragamar shugabancin bankin ga Mista Kabir Adeniyi a matsayin
shugaban rikon kwarya.

Kabir Adeniyi zai jagoranci Bankin ne har zuwa lokacin da
shugaban kasa zai nada cikakken shugaba.

Ahmed Musa Dangiwa, ya gode wa shugabanni da daukacin
ma’aikatan bankin da irin gudumuwar da su ka ba shi har ya iya
cin ma nasarorin da aka samu a lokacin sa, ya na mai cewa ya yi
alfahari da wannan mukami da ya rike.

Daga cikin nasarorin da Ahmed Dangiwa ya samu, akwai bada
rancen kudi Naira biliyan 175 da ya yi ga ‘yan Nijeriya domin
su mallaki gidan kan su, sannan a lokacin da ya ke rike da
Bankin tsakanin shekara ta 2017 zuwa 2022, an samu karin
Naira biliyan 294 a asusun bankin.

Leave a Reply