Home Labaru Martani: Kwanaki 100 Sun Yi Kadan A Gane Kokarin Buhari – Adesina

Martani: Kwanaki 100 Sun Yi Kadan A Gane Kokarin Buhari – Adesina

154
0
Femi Adesina, Mai Magana Da Yawun Shugaban Kasa
Femi Adesina, Mai Magana Da Yawun Shugaban Kasa

Fadar shugaban kasa ta ce, kwanaki 100 sun yi kadan a gane kokarin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, musamman a sabon zangon mulkin sa na biyu.

Mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina ya bayyana haka, yayin da ya ke tattauna da gidan talabijin na Channels, inda ya ce babu yadda za a yi a fara auna gwamnatin a cikin kwanaki 100 saboda ta cigaba daga inda ta tsaya ne.

Adesina ya cigaba da cewa, sabuwar gwamnati kadai ake aunawa da kwanaki 100 na farko, domin hatta a kasar Amurka da Nijeriya ta kwaikwayo tsarin bikin kwanaki 100 na farko ba a auna gwamnatin tazarce da kwanaki 100.

Sai dai Adesina ya ce, gwamnatin Buhari ta ci-gaba da aiwatar da manufofin ta na canji kamar yadda ta fara a wa’adin mulkin ta na farko, ya na mai bugun kirji ya da cewa idan ma za a auna gwamnatin Buhari a ma’aunin kwanaki 100, to sun ciri tuta a bangarorin tattalin arziki da tsaro da kuma manyan ayyuka.