Home Labaru Martani: Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Wa Sanata Abaribe Raddi

Martani: Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Wa Sanata Abaribe Raddi

426
0
Martani: Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Wa Sanata Abaribe Raddi
Martani: Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Wa Sanata Abaribe Raddi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya maida wa Sanata Eyinnaya Abaribe martani, wanda ya bukaci ya yi murabus bisa zargin shi da nuna halin-ko-in-kula a kan tsaron Nijeriya.

A wani martanin gaugawa da shugaba Buhari ya maida ta bakin mai ba shi shawara ta fuskar yada labarai Garba Shehu, ya bayyana kiran da sanata Abaribe ya yi a matsayin shashanci.

Shugaba Buhari, ya ce kamata yayi a ce sanatan ya na gidan Yari, saboda ya kasa kawo shugaban kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu, domin shi ya tsaya ya karbi belin sa.

Garba Shehu, ya ce idan har akwai bukatar shugaba Buhari ya yi murabus, to akwai miliyoyin ‘yan Nijeriya da ya kamata su yi murabus ciki har da shi Sanata Abaribe da ya yi sanadiyyar tserewar Nnamdi Kanu.