Home Labaru Martani: Babu Gwamnan PDP A Yankin Kudu Maso Gabas Da Zai Koma...

Martani: Babu Gwamnan PDP A Yankin Kudu Maso Gabas Da Zai Koma APC – Umahi

220
0
Austin Umahi, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP Na Kasa
Austin Umahi, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP Na Kasa

Jam’iyyar PDP reshen Kudu maso gabashin Nijeriya, ta ce babu ko daya daga cikin Gwamnonin yankin da ke tunanin barin jam’iyyar.

 Mataimakin Shugaban jam’iyyar PDP na kasa Cif Austin Umahi, ya yi watsi da rahoton da aka alakanta da wani shugaban kungiyar matasan kabilar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo Okechukwu Isiguzoro, wanda ya yi ikirarin cewa wasu gwamnonin PDP biyu daga yankin sun kammala shiri sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a Enugu, Umahi ya ce hakan ra’ayin Okechukwu da mukarraban sa ne kawai, tun bayan da aka kunyata su daga kasancewa ainahin jiga-jigan kungiyar Ohanaeze bisa zargin ayyukan da su ka saba ka’ida shekaru kadan da su ka gabata.

Ya kuma gargadi kungiyar ta janye daga yada jita-jitar karya, wanda ka iya shafar martabar shugabannin kabilar Igbo masu mutunci, ciki kuwa har da gwamnonin yankin ta hanyar amfani da sunan kungiyar Ohanaeze.