Home Labarai Martani: Ba Mu Da Niyyar Yin Katsalandan A Dimokraɗiyyar Najeriya

Martani: Ba Mu Da Niyyar Yin Katsalandan A Dimokraɗiyyar Najeriya

51
0

Babban hafsan sojin ƙasa a Najeriya, Janar Taoreed Lagbaja ya
jaddada ƙudurin rundunar soji na kare martabar dimokraɗiyyar
ƙasar.


Da yake yi wa mahalarta taron ƙarawa juna sani kan aiki da hedikwatar rundunar ya shirya a Abuja, Janar Lagbaja ya ce
rundunar ba ta da burin yi wa dimokraɗiyyar ƙasar maƙarƙashiya.


Ya yi kira ga sojojin ƙasar nan su ci gaba da ba da himma wajen gudanar da ayyukansu.


Alƙawarin da Janar Lagbaja ya ɗauka na zuwa ne sakamakon yunƙurin da aka yi na kifar da gwamnati a yankin Afirka ta
yamma da tsakiyar Afirka da suka fuskanci aƙalla juyin mulki bakwai cikin shekara huɗu da ta gabata.


Mali da Guinea da Burkina Faso sai a baya-bayan nan Nijar – dukkansu mambobin ECOWAS sun fice daga ƙungiyar cikin
shekaru huɗu da suka gabata.


Chadi da Sudan da ba sa yankin Afirka ta Yamma suma sun fuskanci juyin mulki a 2021.

Leave a Reply