Home Home Manyan ‘Yan Gadangarƙama Na Shirya Tuggun Kashe Ni – Mele Kyari, Shugaban...

Manyan ‘Yan Gadangarƙama Na Shirya Tuggun Kashe Ni – Mele Kyari, Shugaban NNPC

358
0
Shugaban kamfanin NNPC Limited Mele Kyari, ya ce rayuwar shi ta na cikin hatsari, inda wasu gaggan da sauye-sauyen da ya ke yi a kamfanin man bai yi wa daɗi ba su ke barazanar kashe shi.

Shugaban kamfanin NNPC Limited Mele Kyari, ya ce rayuwar shi ta na cikin hatsari, inda wasu gaggan da sauye-sauyen da ya ke yi a kamfanin man bai yi wa daɗi ba su ke barazanar kashe shi.

Mele Kyari ya bayyana haka ne, a wajen Taron Bitar Ƙa’idoji da Bin Diggigin Ayyuka, wanda Kwamitin Yaƙi da cin hanci da Rashawa na Majalisar Wakilai ya shirya.

Ya ce masu adawa da sauye-sauyen da ake samu a fannonin man fetur, sun koma su na yi ma shi barazanar kashe shi don ya hana su yin abin da su ka ga dama.

Mele Kyari, ya ce ya samu barazanar kisa da dama, amma duk da haka bai damu ba, saboda sun yi amanna cewa babu wanda zai mutu sai lokacin mutuwar shi ya yi.

Leave a Reply