Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, ya rubuta wa hukumar EFCC wasikar korafi a kan zargin da ake yi ma shi na boye biliyoyin kudade a gidan sa da ke Abuja.
Matawalle ya bayyana zargin a matsayin kanzon kurege mara tushe balle makama.
A cikin wata wasika mai dauke da sa hannun lauyan sa Cif Mike Ozekhome, Matawalle ya nanata cewa zargin ba ya da tushe, domin an bude gidan ne da karfin tuwo kuma ba a samu wani abu mai kama da haka ba.
Gwamna Matawalle, ya ce ya kadu matuka da aka janyo hankalin shi zuwa ga wani labari da jaridar Sahara ta wallafa, wanda ya ce an ga biliyoyin naira da aka boye a gidajen Wike da Ganduje da Matawalle.
Matawalle, ya ce a shirye ya ke ya bada damar gudanar da cikakken bincike a kan zargin domin gano gaskiyar lamari.
You must log in to post a comment.