Rahotanni daga jihar Neja na cewa a yanzu haka ƴan bindiga da dama na zaune a cikin gidajen al’ummar garin Allawa ,
kuma su na noma a gonakin su tare da yin anfani da takin zamanin da su ka bari a gidajen su.
Watanni biyar kenan da su ka gabata ƴan bindigar su ka fattataki mazauna garin na Allawa tare da korar su daga matsugunin su kuma su ka mayar da su ƴan gudun hijira.
Wani mazaunin garin wanda ke gudun hijira ya shaida cewa, lamarin ya faru ne bayan da gwamnati ta janye jami’an tsaron da ke basu kariya,
domin a cewar gwamnatin tana so ta canza tsari, sai dai har yanzu ba a mayar da sojojin ba.
Wasu daga cikin su sun yi ƙundinbala, kasancewar halin matsi, sun yi ƙoƙarin leƙawa domin su gani shin gari na komowa, sai dai sun iske abun mamaki, an ƙoƙƙona gidajen su,
sun kuma kwashe takin da suka baro suna amfani da shi a yankin Allawa, yanzu haka ɓarajin suna noma a dajin Allawa.