Home Labaru Kasuwanci Man Fetur: ‘Yan Najeriya Na Da Shakku Kan Binciken Shigo Da Gurbataccen...

Man Fetur: ‘Yan Najeriya Na Da Shakku Kan Binciken Shigo Da Gurbataccen Mai A Ƙasar

163
0

Masu ruwa da tsaki sun fara tsokaci ga iƙirarin gwamnatin Tarayya na cewa za ta gudanar da gagarumin bincike kan batun shigar da gurɓataccen man fetur daga ƙetare zuwa cikin ƙasar.

Timipre Sylva, Karamin Minstan Mai

A jiya Laraba rahotanni suka ambato ƙaramin ministan mai, Timipre Sylva na cewa za a yi bincike don bankaɗo dalilin shigar da gurbataccen man a Najeriya.

Masu motoci da yawa ne suka koka a kan lalacewar ababen hawansu, bayan sun sha man feturin mai yawan sinadarin methanol fiye da kima.

Kafofin yaɗa labaran sun ambato ƙaramin ministan fetur jim kaɗan bayan taron majalisar zartarwar ƙasar na cewa gwamnati ta tashi haiƙan wajen tunkarar batun gurɓataccen man feturin da ya cika gidajen mai.

Ministan ya kuma nemi ‘yan ƙasar su ƙara haƙuri har gwamnati ta kammala bincike kafin a fara batun bayyana sunayen masu hannu

.

Rahotanni sun kuma ambato shi yana cewa kafin yanzu babu wanda ke duba adadin methanol a cikin man fetur ɗin da ake shiga da shi ƙasar.

Lamarin da ya sa wasu ke tambayar da ma ƙasar ba ta da sashen tantance ingancin man da ake shigarwa daga waje.