Home Labaru Mali Na Taron Kasa Kan Neman Shawarwari

Mali Na Taron Kasa Kan Neman Shawarwari

31
0

Gwamnatin Mali da ke karkashin mulkin soja ta kaddamar da taron kasa na kwanaki hudu, kan shirin maida da kasar zuwa mulkin farar hula, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Agustan shekarar 2020.

Yayin kaddamar da bude taron a ranar Litinin da ta gabata, shugaban rikon kwaryar Mali Kanal Assimi Goita, ya ce taron na kasa dama ce ga jama’a don samar da sauyi, ta hanyar gabatar da shawarwarin samar da mafita don kawo karshen matsalolin da kasar ke fama da su.

Sai dai tuni manyan kungiyoyin masu fafutuka da kuma ‘yan adawa suka caccaki taron, tare da shan alwashin kaurace wa halartarsa.

Tarihi dai ya nuna cewar kasar Mali ba ta samun dadewa a karkashin mulkin farar hula tun bayan da ta samu ‘yancin kai daga Faransa a shekara ta 1960.

A watan Agustan shekarar 2020, sojoji a karkashin jagorancin Kanal Assimi Goita suka hambarar da zababben shugaban kasar, Ibrahim Boubacar Keita, bayan zanga-zangar da ya fuskanta tsawon makwanni saboda zargin sa da cin hanci da kuma gaza kawo karshen kungiyoyin ‘yan ta’adda.