Home Labaru Iran Ta Ce Dole Ne A Dage Takunkuman Da Aka Kakaba Mata

Iran Ta Ce Dole Ne A Dage Takunkuman Da Aka Kakaba Mata

134
0

Iran ta ce ya kamata tattaunawar nukiliyar da aka koma a jiya litinin tsakaninta da wakilan manyan kasashen duniya a birnin Vienna, ta mayar da hankali kan batun dage wa kasar takunkumin da aka kakaba mata da kuma tabbatar da cewa Amurka za ta dawo a cikin yarjejeniyar da aka cimma a baya.

Duk da wannan fata na Iran, Kungiyar Tarayyar Turai ta ce tattaunawar abu ne mai cike da sarkakiya.

Tattaunawar ceto yarjejeniyar nukiliyar Iran da aka kulla a shekarar 2015, ta sake komawa a karshen watan Nuwamba, bayan da aka shafe watanni 5 ana tattaunawa bayan zaben shugaban kasar Iran mai ra’ayin rikau Ebrahim Raisi.

Zaman tattaunawar na neman dawo da Amurka ne, bayan ta fice daga yarjejeniyar a shekarar 2018 karkashin shugaba Donald Trump na wancan lokacin tare da kara kakabawa kasar takunkumi.

Gabanin ci gaba da shirin tattaunawar, Ministan Harkokin Wajen Iran Hossein Amir-Abdollahian, ya ce ya kamata a sabunta yarjejeniyoyin da kuma tabbatar da dage takunkumin da Amurka ta kakaba wa kasar sa idan fadar White House ta koma kan wannan yarjejeniya.

Leave a Reply