Home Labaru Makahon Ciniki: Wata Mata Ta Fallasa Yadda Ta Ke Amfani Da Ruwan...

Makahon Ciniki: Wata Mata Ta Fallasa Yadda Ta Ke Amfani Da Ruwan Wanke Gawa A Abincin Sayarwa

1105
0

Wata mata mai sana’ar saida abinci a jihar Akwa Ibom ta haukace, jim kadan bayan ta fallasa yadda ta ke ammfani da asiri domin bunkasa kasuwancin ta.

Matar ta ce ta na gauraya ruwan da aka yi wa gawa wanka a cikin abincin, sannan ta na zuba ruwan da ta wanke gaban ta da jinin haila a cikin abincin da ta ke saidawa.

Ta ce ta na aikata duk wadannan abubuwa ne domin janyo hankalin masu ciniki, a wani mataki na bunkasa kasuwancin ta domin samun kudi.

Bayan ta haukace, matar ta rika guje-guje tsirara ta na ci-gaba da fallasa abubuwan da ta yi, inda wasu daga cikin masu saiyen abincin ciki har da ‘yan achaba su ka far mata da duka, kafin daga bisani jami’an tsaro su ka kai mata dauki.

Leave a Reply