Home Labaru Kishin Kano: Na Sa Kadarori Na Kasuwa Domin Biya Wa Matasa Kudin...

Kishin Kano: Na Sa Kadarori Na Kasuwa Domin Biya Wa Matasa Kudin Makaranta – Kwankwaso

610
0
Rabi’u Musa Kwankwaso, Tsohon Gwamnan Jihar Kano Injiniya

Tsohon gwamnan jihar kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce ya sanya manyan kadarorin da ya mallaka a kasuwa domin ya samu kudin da zai tura matasan jihar Kano karatu a kasashen ketare.

Kwankwaso ya bayyana haka ne, yayi wata zantawa da ya yi da manema labarai a Kano.

Ya ce yanzu haka akwai filayen da Sanata Aliyu Magatakarda Wammako ya ba shi da ya sa a kasuwa, sannan ya sa yawancin filayen da ya mallaka a kasuwa don ya samu kudin da zai biya wa matasa zuwa kasashen waje su yi karatun da za a karu da su, domin ba matasan jihar Kano ilimi ya fi duk kadarorin da ya mallaka.

Kwankwaso ya cigaba da cewa, yanzu haka akwai wasu filayen shi da ke Abuja, da Kaduna da Adamawa da kuma Yobe, wanda a halin yanzu duk ya sa su kasuwa domin ya samu kudin da zai biya wa daliban da za su tafi kasashen waje kudin makaranta.

Leave a Reply