Majalisar wakilai, ta yi kira ga Hukumar Kula da Jami’oi ta kasa da sauran masu ruwa da tsaki su dakatar da duk wasu al’amurran su har sai bayan kammala zaɓe.
Haka kuma, majalisar ta yi kira ga Hukumar Zaɓe ta samar da wani tsari na musamman ga ɗalibai domin su karɓi katin su na zaɓe.
Wannan dai, ya biyo bayan ƙudurin da dan Majalisar Kabiru Ibrahim Tukura ya gabatar a kan bukatar jama’a ta gaugawa yayin tattaunawar kwamitin su.
Kabiru Ibrahim Tukura, ya ce tsarin karatun makarantun gaba da jami’a ya ci karo da tsarin zaɓe, mafi yawan ɗalibai ba za su samu damar yin zaɓen ba, domin makarantu ba su duba ranar zaɓe ba.
You must log in to post a comment.