Majalisar Wakilai ta amince da ƙudirin dokar da za ta haramta
tare da hukunta duk malamin da aka samu da laifin cin zarafi
ko fasikanci da ɗalibai a kwalejoji da jami’o’in Nijeriya.
Tun a shekarata 2020, Majalisar Dattawa ta amince da ƙudirin, amma ya na ƙunshe da tanade-tanade daban-daban.
Shugaban kwamatin kula da harkokin shari’a na Majalisar Dattawa Sanata Opeyemi Bamidele, ya ce taron gamayyar ‘yan majalisar ya haɗa kan tanade-tanaden biyu kafin ya gabatar da rahoton sa a zauren Majalisar.
Daga cikin tanadin dokar, akwai matakan daƙile yunƙurin aikata fasikanci da cin zarafi na jinsi a dukkan matakin karatun gaba da firamare a Nijeriya.
Mataki na gaba shi ne miƙa kundin dokar ga Shugaba Bola Tinubu domin ya sanya mata hannu kafin ta zama doka.