Home Labaru Majalisar Kano Ta Karbi Bukatun Ganduje Kan Masarautu Da Sauran Su

Majalisar Kano Ta Karbi Bukatun Ganduje Kan Masarautu Da Sauran Su

251
0

Majalisar Dokoki ta Jihar Kano, ta amince da kudurin gyara
masarautu na shekara ta 2019 zuwa doka.

Babban Sakataren Yada Labarai na majalisar Uba Abdullahi, ya ce an amince da kudirin ne a zaman babban zauren majlaisar.

Ya ce majalisar ta kuma samu wasika daga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ta neman tabbatar da Mahmoud Balarabe a matsayin shugaban hukumar sauraren korafe- korafe da Yaki da Rashawa ta jihar mai cikakken iko.

Uba Abdullahi ya kara da cewa, majalisar ta mika batun ga kwamitin ta na yaki da rashawa domin ci-gaba da aiki a kai.

Gwamna Ganduje, ya kuma aike wa majalisar daftarin kudirin kafa hukumar kula da hanyoyin karkara, wanda majalisar ta mika wa kwamitin da ya dace domin ci-gaba da daukar matakai.

Leave a Reply