Majalisar Dokoki ta Jihar Kano, ta amince da bukatar Gwamnan Jihar Abba Kabir Yusuf ta neman izinin ya nada masu ba shi shawara na musamman guda 20.
Kakakin Majalisar Ismail Jibrin Falgore ya karanta wasikar bukatar Gwamnan a zauren majalisar, inda aka tattauna a kan wasikar kafin majalisar ta amince da bukatar.
Majalisar ta kuma dage zamanta zuwa ranar 19 ga watan Yuni, a wani kudiri da shugaban masu rinjaye Lawan Husaini Dala ya gabatar, ya kuma samu goyon bayan shugaban marasa rinjaye Labaran Abdul Madari Warawa.
Wannan dai shi ne zama na farko da Majalisar Dokoki ta jihar Kano ta yi bayan rantsar da ita a ranar Talatar da ta gabata.














































