Gwamnatin Tarayya ta ce ta na shirin fara aiwatar da shirin
lamunin dalibai a watan Satumba ko Oktoba na shekara ta
2023.
Babban sakataren ma’aikatar ilimi ta tarayya Andrew David Adejo ya bayyana haka a Abuja, yayin da yake zantawa da manema labarai a kan kudirin dokar da shugaba Tinubu ya sanya wa hannu.
Shugaba Bola Tinubu dai ya amince da kudirin lamunin dalibai domin cika alkawarin da ya dauka a lokacin yakin neman zabe, wand ya tanadi lamuni marasruwa ga daliban Nijeriya marasa galihu.
Andrew David Adejo, ya ce a takaice dokar ita ce samar da hanyoyin samun ilimi mai sauki ga ‘yan Nijeriya marasa galihu, ta hanyar ba da lamuni maras ruwa daga asusun lamuni na ilimi a Nijeriya.