Majalisar Dokokin jihar Kano ta amince da dokar kafa masarautu uku masu daraja ta biyu-biyu.
A yayin zamanta na yau Talata ne majalisar ta yi wa dokar karatu na biyu da na uku kafin ta amince da ita.
Sabuwar dokar ta tanadi Gaya, da Ƙaraye, da Rano a matsayin ƙananan masarautu kuma dukan su za su kasance ne a ƙarƙashin Masarautar Kano.
Masarautar Rano na da ƙananan hukumomi uku na Rano, da Bunkure, da Kibiya, sai Masautar Ƙaraye dake da biyu, wato Karaye da Rogo,
yainda ita kuma Gaya ke da uku ita ma, da suka kunshi Gaya, da Ajingi, da kuma Albasu.