Home Labarai Majalisar Dattawa Ta Ba Hafsoshin Tsaro Wata Hudu Su Kawo Karshen Rashin...

Majalisar Dattawa Ta Ba Hafsoshin Tsaro Wata Hudu Su Kawo Karshen Rashin Tsaro

75
0

Majalisar Dattawa ta ba manyan hafsoshin tsaron Nijeriya wa’adin watanni hudu su kawo karshen matsalolin tsaron da ke addabar sassan kasar nan.

Wannan dai ya na zuwa ne, bayan majalisar ta yi doguwar ganawa da shugabannin tsaron duk da cewa ta na hutu.

A baya-bayan nan dai, lamurran tsaro sun sukurkuce, lamarin da ya kai ga wasu ‘yan majalisar yunkurin tsige Shugaba Muhammadu Buhari muddin bai sauya salo ba.

Majalisar dokoki ta bayyana tsoro da damuwar ta game da ƙaruwar rashin tsaro a Nijeriya, musamman harin da ‘yan ta’adda su ka kai kwanan nan a Abuja.

Shugaban majaliar dattawa Sanata Ahmad Lawan, ya kira shugabannin tsaro taron gaugawa wanda ya kasance lamari mai ban tsoro.

A wajen taron, sanatoci sun ba shugabannin tsaro shawarwari a kan yadda za a kare Birnin Abuja da ma Nijeriya baki daya.