Home Labaru Majalisa Za Ta Amshi Jerin Sunayen Ministoci Ranar Alhamis – Shugaban Masu...

Majalisa Za Ta Amshi Jerin Sunayen Ministoci Ranar Alhamis – Shugaban Masu Rinjaye

102
0

Shugaban masu rinjaye na majalisar Dattawa Sanata Michael
Opeyemi Bamidele, ya ce Majalisar za ta karbi jerin sunayen
ministocin shugaba Tinubu da ake ta jiran tsammani nan da
kwanaki biyu masu zuwa.

Sanata Bamidele ya bayyana haka ne, a wajen wani taron lacca na bikin murnar zagayowar ranar haihuwar sa da kaddamar da littafin sa na ‘Diamond Jubilee’ a Abuja, inda ya ce shugaba Tinubu da kan sa ya shaida fada ma shi haka lokacin da ya buga ma shi waya domin taya shi murnar cika shekaru 60 da haihuwa.

Ya ce shugaba Tinubu ya kira shi ta wayar tarho da misalin Mkarfe 10:03 na safe, inda ya ce ba zai samu damar halartar bikin ranar haihuwar sa ba, saboda shirin mika wa majalisar dattawa jerin sunayen ministoci nan da sa’o’i 48 masu zuwa.

Leave a Reply