Kotun Daukaka Kara da ke Abuja, ta wanke tsohon Gwamnan
Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido da ‘ya’yan sa biyu daga
zargin rub-da-ciki a kan wasu kudade.
Kotun, a karkashin jagorancin Mai Shari’a Adamu Waziri, ta ce Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ba ta da hurumi sauraren karar da aka shigar a kan lamarin tun farko, saboda kusan duk abubuwan da ake kara a kan su a wajen yankin ta aka aikata.
Babbar kotun dai ta ki amincewa da karar da aka shigar gaban ta a kan lamarin tun farko, inda daga nan ne Sule Lamido ya daukaka kara a gaban kotun ya na kalubalantar hukuncin da kotun baya ta yanke.
An dai gurfanar da Sule Lamido ne a gaban Mai Shari’a Adeniyi Ademola bisa zarge-zarge 43 a shekara ta 2016, wadanda su ka shafi hada baki da kuma wasa da aiki a kan kudin da yawan su ya kai Naira biliyan 1 da miliyan 351.
Idan dai baa manta ba, an gurfanar da Sule Lamido ne tare da ‘ya’yan sa biyu Aminu da Mustapha, sai kuma Wada Abubakar da wasu kamfanoni guda hudu.