Home Labaru Majalisa Ta Yi Tir Da Yadda Jama’In Kwastam Ke Buɗe Wa Jama’a...

Majalisa Ta Yi Tir Da Yadda Jama’In Kwastam Ke Buɗe Wa Jama’a Wuta Ba Bisa Ƙa’ida Ba a Katsina

65
0

Majalisar Dattawa ta yi Allah-wadai da buɗe wutar da wasu
jami’an hukumar kwastam su ka yi a kan mutanen da ba su ji
ba su gani ba a Jihar Katsina, don haka ta buƙaci hukumar ta
gudanar da bincike a kan lamarin.

Sanata Abdul’Aziz Musa ‘Yar’adua ne ya gabatar da kudirin a zauren majalisar, inda ya buƙaci ta gaggauta gudanar da bincike a kan yadda jami’an Kwastam a jihar Katsina ke amfani da makamai ba bisa ƙa’ida ba.

Ƙudurin dai ba ya rasa nasaba da harbe-harben da jami’an hukumar Kwastam su ka yi a ranar Asabar da ta gabata, inda wasu jami’an hukumar su ka buɗe wa Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Jihar Katsina Alhaji Jabir Tsauri wuta a garin Gorar ‘Yammama da ke ƙaramar hukumar Malumfashi a kan hanyar shi ta zuwa Kaduna.

Da farko dai an yi zargin ‘yan bindiga ne su ka buɗe wa motar Shugaban ma’aikatan wuta, kasancewar jami’an hukumar su na sanye da farin kaya, lamarin da ya tilasta ma shi tserewa shi da direban sa domin tsira da ran su.

A na shi bangaren Gwamnan Jihar Katsina Dikko Umar Raɗɗa ya nuna damuwa da yadda jami’an hukumar Kwastam ke harbin al’umar jihar ba tare da sun aikata wani laifi ba, inda ya buƙaci hukumomin tsaro su binciki musabbabin harin cikin gaugawa.

Leave a Reply