Wasu masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC na yankin
Kudu maso gabashin Nijeriya, sun ja kunnen Shugaba
Bola Ahmed Tinubu dangane da rabon mukamai.
Kungiyar ta magoya bayan jam’iyyar APC, ta tunatar da shugaba Tinubu cewa mutanen Legas kawai su ke tashi da mafi rinjayen mukaman da ya ke rabawa.
Haka kuma, kungiyar ta ce ana ware sauran jihohin bangaren ana fifita Legas wato inda shugaba Bola
Ahmed Tinubu ya fito.
Shugaban kungiyar Otunba Dele Fulani, ya ce sun damu da yadda abubuwa su ke tafiya, kuma su na tsoron hakan ta faru wajen nadin Ministoci da sauran ma’aikatu.
Otunba Dele Fulani, ya ce kungiyar ta lura cewa a cikin hadimai 20 da shugaban Tinubu ya nada a kwanakin baya, akalla 13 daga cikin su daga yankin Legas su ke.