Home Coronavirus Majalisa Ta Jefa Kwangilolin Bogi A Kasafin NDDC

Majalisa Ta Jefa Kwangilolin Bogi A Kasafin NDDC

544
0
Majalisa Ta Jefa Kwangilolin Bagi A Kasafin NDDC
Majalisa Ta Jefa Kwangilolin Bagi A Kasafin NDDC

Shugaban rukon kwarya na hukumar kula da harkokin yakin Neja Dalta NDDC Farfesa Kemebradikumo Pondei, ya zargi ‘yan majalisar tarayya yin cushe a cikin kasafin hukumar  na shekara ta 2019.

Pondei ya bayyana hgaka ne ga manema labarai, tare da cewa  an cusa kwangilolin bogi kimanin 500 a kasafin 2019.

Shugaban ya kara da cewa, sun gano ta’adin ne lokacin da su ka binciki kasafin kudin 2019, kuma ‘yan majalisa ne suka jirkita kasafin da aka aika masu.

Farfesa Pondei ya bayyana haka ne a matsayin martani game da zargin da ake yi masa wa yin awon gaba da wasu kudade.

Idan dai ba a manta ba, shugaba Muhammadu Buhari ya bada umarnin a binciki kudin da aka kashe a hukumar NDDC, wanda hakan zai sa a bankado duk wata barnar da jami’an hukumar su ka tafka.

Sai dai shugaban hukumar Farfesa Pondei ya ce babu wani kwangilar kirki da NDDC ta yi, sai dai kawai an bar hukumar da wasu kananan ayyuka.

Leave a Reply