Home Home Buhari Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Na Karshe A Gwamnatin Sa

Buhari Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Na Karshe A Gwamnatin Sa

278
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya jagoranci zaman majalisar zartarwa ta kasa da aka saba yi duk mako a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Buhari ya dawo Nijeriya bayan tafiyar da ya yi zuwa London domin halartar bikin nadin Sarki Charles III.

Zaman majalisar dai shi ne na karshe da shugaba Buhari zai jagoranta, inda a mako mai zuwa za a yi bankwana da gwamnatin sa.

Daga cikin wadanda suka halarci zaman majalisar, akwai mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, da mai ba shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro Babagana Monguno.

Manyan ministocin da su ka halarci zaman kuma sun hada da na harkokin cikin gida Rauf Aregbesola, da na kimiyya da fasaha Olorunimbe Mamora, da ministar kudi Zainab Ahmed, da na sufuri Mu’azu Sambo, da na kiwon lafiya Dakta Osagie Ehanire, da na sadarwa Farfesa Isa Pantami.

Sauran sun hada da ministan wasanni Sunday Dare da na sufurin jiragen sama Hadi Sirika, da na muhalli Mohammed Abdullahi, da na ayyuka Babatunde Fashola, da na birnin Abuja Mohammed Bello, da na harkokin ketare Geoffrey Onyeama da Atoni-Janar na tarayya Abubakar Malami.

Leave a Reply