Home Home Mai Bada Shaidar Atiku Ya Ce Inec Ta Goge Sakamakon Zaɓen Da...

Mai Bada Shaidar Atiku Ya Ce Inec Ta Goge Sakamakon Zaɓen Da Ke Cikin Na’urar BVAS

390
0

Wani mai bada shaida a shari’ar zaɓen shugaban ƙasa na Atiku Abubakar da jam’iyyar PDP, ya shaida wa alƙalan kotun cewa hukumar zabe ta goge duk sakamakon zaɓen da ke cikin Na’urar BVAS.

Mai bayar da shaida Hitler Nwala, wanda ƙwararren masanin sarrafa na’urorin zamani ne, ya shaida wa kotu cewa ya bibiyi na’urorin BVAS 110 da aka yi zaɓe da su a birnin Abuja, amma ya samu duk hukumar zabe ta goge sakamakon zaɓen da ke cikin su.

Lauyan Atiku Abubakar Chris Uche ne ya gabatar da mai bada shaidar a gaban kotun.

Idan dai ba a manta ba, a makon da ya gabata an gabatar da Dino Melaye a matsayin mai bada shaida, inda ya rantse a gaban kotu cewa an yi ƙwange da aringizon sakamakon zaɓe domin a kada Atiku.

Leave a Reply