Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya janye rushe Hukumomin Gudanarwa na Hukumar hana sha da fataucin miyagun Ƙwayoyi NDLEA, da Hukumar Kula da Ingancin Abinci da magunguna ta Ƙasa NAFDAC.
Wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya Willie Bassey ya fitar, ta ce Hukumomin biyu ba su cikin waɗanda aka rusa.
Haka kuma, shugaba Tinubu ya maida Hukumar NEMA da NAHCON a ƙarƙashin Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, kamar yadda dokar Nijeriya ta ce a can za su kasance tun farkon kafa su.














































