Home Home Mahara Sun Sace Basarake Da Matarsa A Kogi

Mahara Sun Sace Basarake Da Matarsa A Kogi

93
0

‘Yan bindiga sun sace wani basaraken Idofin da matar sa a hanyar Makutu zuwa Idofin da ke ƙaramar hukumar Yagba ta gabas a jihar Kogi.

Shaidu sun bayyana wa manema labarai cewa, da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin ranar Litinin da ta gabata ne maharan su ka sace basaraken mai suna Shedrack Durojaye Obibeni da matar sa.                  

Maharan masu ɗauke da muggan makamai sun kafa shingen bincike ne a kan hanyar, inda su ka yi awon gaba da basaraken da matar sa zuwa cikin daji.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kogi SP William Aya ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni ‘yan sanda sun bi sahun maharan domin ceton basaraken da matar sa.

Leave a Reply